A ranar 11 ga wata, a yayin taron kwamitin Asiya na birnin New York, mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka ta fuskar tsaro Thomas Donilon, ya yi jawabi da ke da lakabin "Manufar kasar Amurka game da yankunan Asiya da tekun Fasific", inda ya ce, dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, na da muhimmancin gaske cikin manufar daidaita manufofin da ke da nasaba da kasashen Asiya da tekun Fasific da Amurka ke yi a yayin wa'adin aiki na biyu na shugaba Obama. Donilon ya bayyana cewa, a farkon wannan wa'adi na biyu na shugaban Obama, za a kammala aikin canja shugabannin kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta shiga wani sabon mataki, a sa'i daya kuma, hakan na nuna kasancewar sabuwar dama da kuma kalubale a gabansu. Nan gaba, Sin da Amurka za su ci gaba da hadin gwiwarsu ko da kasancewar sabane-sabane a tsakaninsu.
Donilon ya kuma yi watsi da batun zargin zaman doya da manja, ko sa-in-sa tsakanin manyan kasashen biyu da ake yi, yana mai ganin batu ne maras tushe. Kuma ya musunta zargin cewa wai Amurka na da niyyar nuna rashin amincewa ga bunkasuwar kasar Sin. Ya jaddada cewa, inganta dangantaka a tsakanin bangarorin biyu cikin yakini ya zama babban buri na shugabannin kasashen Sin da Amurka.
Donilon ya jaddada cewa, sakamakon kara dogaro ga juna ta fuskar tattalin arziki, kamata ya yi kasashen Amurka da Sin, su inganta hadin gwiwarsu a wannan fanni. Bugu da kari, a wannan lokacin da Amurka ke nuna goyon baya ga aikin canja salon raya tattalin arziki da kasar Sin ke yi, tana neman yin kokari tare da Sin wajen tabbatar da hada-hadar kudi, da tinkarar sauyin yanayi, da warware rikicin makamashi da sauran batutuwan duniya.(Bako)