in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Sin da Amurka su yi hadin gwiwa
2013-05-29 16:34:52 cri

Za a yi ganawa tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Amurka Barack Obama a ran 7 zuwa 8 ga watan Yuni a gandun noma na Annenberg, wanda zai jawo hankali kasa da kasa, kuma tsarin da za a bi a wannan karo ba a taba ganin irinsa ba tun shekaru fiye da 30 na bayan kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen 2. Game da wannan batu, sashin kula da labarin kasashen waje na jaridar People's Daily ya rubuta wani sharhi a yau 29 ga wata cewa, ya kamata, Sin da Amurka su hada kai a tsakaninsu domin kawo moriyar juna.

A sabon halin da ake ciki, abin da ya fi muhimmanci shi ne kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu nan gaba. Bugu da kari, yin musayar ra'ayi kai tsaye tsakanin shugabannin biyu zai taimakawa kasashen biyu wajen tsara taswirar raya da ba da tabbaci ga dangantakar hadin kai tsakaninsu.

Sharhin ya ce, kasashen biyu za su kawo moriyar juna, muddin suka hada kai a tsakaninsu. Saboda haka, Amurka ta amince da matsayin da Sin ta kan dauka na kulla sabuwar dangantakar abokantaka tsakaninsu, abin da ya shaida cewa, kasashen biyu duk sun fahimci hakkin tarihi dake bisa wuyansu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China