Mr Barnett tsahon wakilin asusun IMF a kasar Sin ya nuna cewa,a halin yanzu kasar Sin ta kara sa lura kan gyaran tsari, ba matakan sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki na gajeren lokaci ba. Wannan ya bayyana cewa, shugabannin kasar Sin sun himmatu wajen kyautata tsarin samun bunkasuwar tattalin arziki cikin daidaici da dorewa.
Ban da wannan kuma, yana sa ran cewa, ta hanyar canja tsarin samun bunkasuwar tattalin arziki, Sin za ta kara samun bunkasuwa, ta yadda za a kara samar da aikin yi, kara yawan kudin shiga da jama'a ke samu da yawan kudin da ake kashewa, da kuma rage yawan albarkatun kasa da ake amfani da su, da kuma kiyaye muhalli. (Zainab)