Kasar Sin ta yi kira ga sassa daban daban na Sham da su warware rikici ta hanyar yin tattaunawa
Ranar Litinin 30 ga wata, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yi kira ga sassa daban daban na kasar Syria masu ruwa da tsaki da su tsagaita bude wuta cikin hanzari, a kokarin warware rikicin kasar ta hanyar yin tattaunawa.
Hong Lei ya kara da cewa, kullum kasar Sin na ganin cewa, warware batun Syria a siyasance, ita ce hanya daya kacal da za a iya bi. Don haka kasar Sin za ta ci gaba da yin iyakacin kokarinta tare da sauran kasashen duniya wajen aiwatar da kudurori da shawarwarin da abin ya shafa, a kokarin ba da gudummowa a fannin warware batun na Syria yadda ya kamata daga dukkan fannoni kuma cikin dogon lokaci.(Tasallah)