in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an Amurka da Rasha za su tattauna kan batun makamai masu guba na kasar Sham
2013-09-12 14:19:42 cri

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta sanar a ran 11 ga wata cewa, sakataren harkokin waje John Kerry zai tashi zuwa birnin Geneva na Switzerland, inda zai gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov tsakanin ranar alhamis 12 zuwa juma'a 13 a kan makamai masu guba na kasar Sham.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Jen Psaki ta bayyana a wannan rana cewa, wasu masana za su rufa wa John Kerry baya a lokacin ziyararsa a wannan karo, wadanda za su yi shawarwari tare da masanan kasar Rasha a fannin kimiyya da fasaha, domin fitar da wani mataki da ya dace ta fuskar kimiyya wajen murkushe wasu makamai masu guba a kasar Sham.

Babbar jami'ar kungiyar kawancen kasashen Turai wato EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro Catherine Ashton ta ba da sanarwa a ran 11 ga wata, inda ta yi maraba da shawarwarin da Rasha ta gabatar, wanda ya nemi kasashen duniya da su sa ido kan na'urorin makamai masu guba a kasar Sham, tare kuma da fatan cewa, shawarwari zai kasance mataki mai amfani wajen warware rikicin kasar Sham.

Shugaban kasar Turkiya Abdullah Gül kuwa ya bayyana a ran 11 ga wata cewa, Turkiya na maraba da shawarar Rasha. Ban da haka, firaministan kasar Italiya Enrico Letta shi ma, ya nuna a wannan rana cewa, akwai lokaci da kuma sharadu ga MDD da ta shiga tsakanin wannan rikici kafin aka dauki matakin soja kan kasar Sham. Italiya ba za ta dauki matakin soja ba ko kadan idan dai ba bisa ka'idar MDD ba.

Hakazalika, a ran 10 ga wata, kakakin kungiyar adawa ta kasar Sham Khalid Saleh ya bayyana a birnin Washington cewa, Amurka ta rigaya ta samar musu wasu manyan makamai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China