Sojin gwamnatin kasar Sham sun sanar a ran 19 ga wata cewa, sun kwato wani muhimmi wuri dake tsakiyar kasar wato garin al-Qussair, ta yadda za ta sassauta halin da ake ciki a birnin Homs a wannan yanki ta fuskar tsaro.
Kamfanin dillanci labaru na kasar ya ba da labarin cewa, sojin gwamnatin kasar Sham ya kewaye wannan gari a wannan rana da sassafe, inda 'yan tawaye suka boye, daga baya sun daga tutar kasar a cibiyar garin. Sojin gwamnatin sun bukaci jama'a dake zaune a wannan gari da su bar gidajensu domin kaucewar samun asara.
'Yan tawaye sun mamaye wannan gari tun daga shekarar bara, wanda ya ke dab da kasar Lebanon, da muhimmin birnin Homs, da kuma babbar hanyar motoci da ta hada Homs da Damascus, saboda haka garin al-Qussair ya zama wani muhimmin wuri da ake kokarin mamayewa cikin artabun da aka yi tsakanin bangarori 2 masu jayayya da juna na kasar Sham.
Ban da haka, kamfanin dillancin labaru na kasar ya ce, sojin gwamnatin kasar sun mamaye wani yankin dake karkarar birnin Damascus, sannan sun harbe 'yan tawaye fiye da goma. (Amina)