Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci bangarori daban daban na Siriya dasu bada hadin kai wajen isar da taimakon jin kai
Kwamitin sulhu na MDD ya yi kira a ranar Labara ga dukkan bangarori daban daban na kasar Siriya da su gaggauta daukar matakan da suka wajaba domin kara yawaita ayyukan kai taimakon jin kai da kuma taimakawa wajen isar da agaji a cikin kasar dake fama da yaki. A cikin sanarwar shugaban kwamitin na wannan watan Oktoba, jakadan kasar Azerbaidjan mista Agshin Mehdiyev, a madadin kwamitin sulhu na MDD ya jaddada matsalar jin kai ta yi tsanani dalilin rikicin da kasar take fama da shi na bukatar a gudanar da aikin gaggawa da zai taimaka wajen kawo sauki wajen isar da taimako yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba a dukkan fadin kasar. Bisa nuna damuwa kan cigaban tashin hankali dake tsanani da kuma mutuwar mutane fiye da dubu dari da lalacewar yanayin jin kai a cikin wannan kasa, kwamitin tsaro na MDD yayi kira ga dukkan bangarori dake gaba da juna dasu kawo karshen bude wuta da kuma dakatar da duk wasu ayyukan keta hakin dan adam. Haka kuma sanarwar ta yi kira ga bangarorin da su kaucewa kai hari kan gine ginen fararen hula da kuma girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma kiyaye hanyoyin da ake amfani da su domin kai agajin jin kai zuwa ga mutanen kasar dake cikin bukata. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku