Sojojin gwamnatin kasar Sham sun sanar a ran 23 ga wata cewa, sun samu ci gaba ta fannin ayyukan da suke gudanarwa a wasu wurare da dama, ciki hadda yankin Balza dake birnin Damascus.
Ban da birnin Damascus da yankunan dake kusa da shi, sojojin gwamnatin kasar na ci gaba da yin musayar wuta da masu dauke da makamai na tsagin 'yan adawa, dama sauran 'yan ta'adda da suka fito daga kungiyar Jabhat Al-Nusra Front da sauran kungiyoyin masu tsattsauran raayi masu tsattsauran ra'ayi a lardin Aleppo, Homs da dai sauran lardunan kasar. (Amina)