A ran 10 ga wata bisa agogon wurin, kwamitin sulhu na MDD ya amince da shawara da babban sakatare Ban Ki-moon ya gabatar, wato MDD za ta kafa wata tawagar hadin gwiwa tare da kungiyar haramta makamai masu guba ta duniya, domin sa ido kan yunkurin lalata makamai masu guba a Sham.
Bisa shirin Ban Ki-moon, an ce, daga ranar 1 ga watan gobe, tawagar za ta shiga cikin aikinta na wa'adi na uku, wato lokacin da take fi gamuwa da matsaloli ne, daga lokacin, tawagar za ta fara shiga cikin hakikanin aiki na sa ido da kuma tabbatar da aikin lalata makamai masu guba, lallai, za a gama dukkannin ayyuka ne kafin ranar 30 ga watan Yuni na shekara mai zuwa. Ban Ki-moon ya ce, wannan aiki ba kawai ya bukaci goyon baya daga gwamnatin Sham ba, har ma ya bukaci goyon bayan daga mambobin MDD. Game da haka, kasar Sin ta ce tana son tura kwararru don yin ayyuka da abin ya shafa, kuma idan akwai bukata za ta ba da taimakon kudi.(Danladi)