Har ila yau kasar ta Sin na fatan kasashen duniya za su cimma daidaito, wajen marawa shirin gudanar da ci gaban babban taron birnin Geneva baya.
A ranar Jumma'a 27 ga watan nan ne dai aka kada kuri'ar amincewa da kuduri mai lamba 2118, wanda ya tanaji raba kasar ta Siriya da dukkanin makamanta masu guba. Hakan kuwa ya biyo bayan amincewar da hukumar lura da makamai masu guba ta kasa da kasa OPCW ta yi, da shirin lalata tarin makamai masu guda da Siriyan ta mallaka nan da shekarar 2014.
Da yake karin haske kan wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce dukkanin wakilan kwamitin tsaron na gaggawar ganin an warware batun kasar Siriya ba tare da bata wani lokaci ba, matakin da ya ce ko shakka babu zai taimaka wajen maido da yanayin zaman lafiya, tare da ba da damar warware rikicin kasar cikin lumana
Wan Yi ya ce babu wata kasa dake gabas ta tsakiya ciki hadda ita kanta Siriya dake iya jurewa yaki, don haka bin matakan diplomasiyya ne hanyar warware dukkanin wani sabani daka iya wakana.
Ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya kuma kara da cewa, wajibi ne kwamitin tsaron MDD ya sanya lura matuka kan dukkanin wani nau'in mataki da zai dauka kan batun Siriya, kasancewar matsayarsa na iya shafar rayuwar al'ummar kasar, da ma ragowar sassan duniya baki daya. (Saminu Hassan)