in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi kira ga matasa da su taka rawa wajen samun ci gaba mai dorewa a duniya
2013-08-08 15:39:16 cri

Babban sakantaren MDD Mr Ban Ki-Moon ya yi kira ga matasan duniya a ran 7 ga wata cewa, ya kamata, matasa su dukufa kan gaggauta manufar raya kasa da MDD ta tsayar a shekarar 2000 da tsai da ajandar raya duniya bayan shekarar 2015 domin tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa nan gaba.

An kira babban taron matasa karo na 12 na kasa da kasa a wannan rana a hedkwatar MDD da ke birnin New York.

Ban Ki-Moon ya ce, ya kamata matasa su dauki nauyin dake wuyansu domin ba da gudummawa wajen samun ci gaba mai dorewa. Ban da haka, ya bukaci matasa da su kara himma wajen dukufa kan tinkarar wasu kalubaloli, ciki hadda warware batun rashin aikin yi da sa kaimi ga samar da adalcin zaman al'umma da sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China