A lokacin ganawar,Wang Yi ya nuna cewa, a matsayin wata kungiyar kasa da kasa mai fadi a ji, MDD tana taka wata muhimmiyar rawar da ba wanda zai maye gurbinta ba a cikin wasu batutuwan kasa da kasa kullum. Sin tana goya bayan MDD, kuma ta mai da tsarin dokokin MDD a matsayin ginshikin daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, tare kuma da dukufa kan kiyaye zaman oda da doka na duniya bisa tsarin dokokin MDD.
A nasa bangare, Ban Ki-Moon ya ce, Sin tana taka rawar jagoranci cikin harkokin kasa da kasa gwargwadon karfinta, kuma ta ba da babbar gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro, da samun bunkasuwa mai dorewa.
Don haka MDD ta nuna gare ta yabo kuma tana fatan Sin zata ci gaba da ba da taimako ga aikin kiyaye zaman lafiya da MDD ke gudanarwa, sa'anan su kara hadin gwiwa tsakaninsu don tinkarar kalubaloli ta kowane fanni tare. (Amina)