Mr. Ban yana jawabi ne a lokacin babban taron Majalisar game da Somaliya bayan ziyarar sa na kwanannan da ya kai kasar da kuma sansanin 'yan gudun hijiran na Dadaab dake makwabta da su a Kenya wadanda ke dauke da dubban 'yan gudun hijira daga Somaliya.
A yayin da yake Dadaab, Mr. Ban ya gana da 'yan gudun hijira da suka tsere daga Somaliya a dalilin fari da kuma fadace fadace da ake ta yi tsakanin gwamnati da 'yan kungiyar nan ta Al-Shabaab masu fafutukar son jan ragamar mulkin kasar da yaki ya daidaita.
Ya sanar da taron cewa, '' Ranar Litinin, an sake samun fashewar wani na'u'ra a sansanin Hagadera, inda mutum daya ya mutu'', ya kara da cewa, ''A talatan nan kuma wani na'u'ran da bai kai girman sauran ba ya fashe kusa da wata kasuwa dake dab da sansanin Ifo, kuma duk da Ifo da Hagadera suna cikin sansanin Dadaab ne, tsoron irin wadannan hare hare babban abin damuwa ne ga 'yan gudun hijiran dake tsugunne a wadannan sansanoni daya iske a Dadaab', inji Mr. Ban. (Fatimah)