in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki Moon ya sa kaimi ga bangarori biyu da ke rikici da juna na Mozambica da su daidaita bambancin ra'ayoyinsu ta hanyar yin shawarwari
2013-10-24 17:06:30 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya bayar da wata sanarwa ta kakakinsa a ran 23 ga wata da dare, cewar yana sa ido akan halin da ake ciki a kasar Mozambica, a sa'I daya kuma yana sa kaimi ga bangarori biyu da ke rikici da juna na Mozambica da su daidaita bambancin dake tsakanin su ta hanyar yin shawarwari.

Sanarwar ta ce, Ban Ki Moon yana mai da hankali sosai kan karuwar rikicin nuna karfin tuwo da ke tsakanin sojojin gwamnatin Mozambica da jam'iyyar adawa wato Mozambican National Resistance, RENAMO, Ban Ki Moon ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da kada su dauki matakai da mai yiyuwa zai kawo barazana ga zaman lafiya da zaman karko a kasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Ban Ki Moon yana sa kaimi ga bangarorin biyu da ke rikici da juna da su aiwatar da shawarwarin da ke kunshe da bangarori daban daban, su daidaita bambancin ra'ayinsu bisa tsarin dimukuradiyya na yanzu, kuma su tabbatar da cewa, kasar Mozambica za ta kara kokari wajen cimma burin samun sulhuntawa a al'umma da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci.

A ran 21 ga wata, sojojin gwamnatin Mozambica suka kai farmaki ga sansanin cikin daji inda shugaban Jam'iyyar RENAMO Afonso Dhlakama ke zama a boye inda suka mamaye wurin, sai dai Dhlakama ya tsire. Sakamakon haka Jam'iyyar RENAMO ta sanar da cewa ba za ta ci gaba da bin yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da ta daddale da gwamnati ba, kuma ta ce, mai yiyuwa ne hakan zai kawo karshen zaman lafiya a Mozambica.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China