Bayan da ya yi wannan tsokaci ranar Laraba yayin da ya kaiwa tsohon shugaban ziyarar girmamawa, ya kara da cewa, a wannan lokaci da ake mika sakwannin fatan alheri ga Mandela, bisa cikarsa shekaru 95 da haihuwa, ya zama wajibi kuma a dauki matakan da suka wajaba, domin kyautata rayuwar al'umma. Cikin wata sanarwa dake kunshe da sakon nasa, Mr. Ban ya yi kira ga al'ummar duniya da ta yi amfani da a kalla mintuna 67 a yau Alhamis, domin aiwatar da ayyukan tallafawa rayuwar bil'adama, a matsayin wani mataki na karrama tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu, wanda ya kwashe shekaru 67 na rayuwarsa yana hidima ga ci gaban rayuwar al'umma, da kare hakkin bil'adama, tare da tabbatar da adalci.
MDD ce dai ta ware wannan rana ta 18 ga watan Yunin ko wace shekara, cikin shekarar 2007, domin tunawa da irin dinbin gudummawar da Mandela ya baiwa ci gaban rayuwar bil'adama. (Saminu Alhassan Usman)