in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bayyana jin dadinsa saboda zaben kasarsa cikin kwamitin sulhu na MDD
2013-10-18 15:23:19 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana jin dadi da farin-ciki sosai game da zaben kasarsa cikin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 17 ga wata.

A cikin kuri'u 193 da aka kada, Najeriya ta samu kuri'u 186. A cikin wata sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mista Reuben Abati ya bayar, Jonathan ya nuna godiya ga dukkan kasashen da suka goyi bayan Najeriya, inda ya ce, nasarar da kasar ta samu na zama membar da ba ta dindindin ba a cikin kwamitin sulhun MDD, zata taimaka mata wajen kara taka rawa ta fuskar tabbatar da zaman lafiya, tsaro da daidaita harkokin siyasa a nahiyar Afirka, har ma a duniya baki daya.

Jonathan ya kuma lashi takobin cewa, a karkashin mulkin gwamnatinsa, Najeriya za ta ci gaba da bada gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya mai dorewa a fadin duniya.

Bayanai na nuna cewa, wannan shi ne karo na hudu da aka zabi Najeriya don ta zamanto membar da ba ta dindindin ba a cikin kwamitin sulhu na MDD, tun da ta samu 'yancin kai a shekara ta 1960.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China