in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon zai kawo ziyara kasar Sin a mako mai zuwa
2013-06-13 15:31:47 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon zai kai ziyarar aiki na tsawon kwanaki hudu a nan kasar Sin a ran 17 ga wata. Yayin ziyarar tasa, Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar Sin, Xi Jinping, firaministan kasar Li Keqiang, wakilin majalisar gudanarwa mai kula da harkokin waje Yang Jiechi da kuma ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi domin tattauna wasu manyan batutuwa dake jawo hankalinsu.

Mataimakin kakakin Mr Ban Ki-Moon, Eduardo del Buey ya fadi a ran 12 ga wata a gun taron manema labaru da aka yi a birnin New York hedkwatar MDD cewa, Ban Ki-Moon zai ziyarci wata cibiyar horar da sojan kiyaye zaman lafiya dake birnin Beijing karkashin jagorancin ma'aikatar tsaron kasar, da taron tattauna kan makamashi mara gurbata yanayi da kungiyar yin tsimin makamashi da samar da kayayyaki ba tare da gurbata muhalli ba za ta shiya, sa'annan zai gana da mataimakin direktan kwamtin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Xie Zhenhua.

An ba da labari cewa, Ban Ki-Moon zai iso birnin Beijing a ran 18 ga wata, wanda ya kasance ganawarsa ta farko da sabbin shugabannin kasar Sin bayan kama aiki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China