Kwararru sun shiga cikin wa'adi na biyu na aikinsu da ya shafi aikin yin bincike da kuma kwance makamai masu guba, har ma da lalata su.
Ta wani bangare, kamfanin dillancin labaru na Sham ya bayar da wani labari cewa, a ran nan, sojojin gwamnati sun kai samame tare raunana wasu mayakan kungiyar 'Jabhat al-Nusra Front' a yankunan Al-kabon da Jobar da dai sauransu, tare da lalata makamansu.
Ahmad al-Jarba, shugaban kungiyar dake adawa da gwamnatin Assad da ke wajen kasar Sham, ya bayyana a ran 7 ga wata cewa, 'yan adawa sun yarda da halartar taron duniya na biyu da za a gudana a birnin Geneva kan batun Sham. A sa'i daya kuma, Ahmad al-Jarba ya ce, sam 'yan adawa ba za su yi shawarwari da gwamnatin Bashar al-Assad ba, sun bukaci da ya sauka daga mukaminsa. (Danladi)