Rukunin kwararru na MDD da hukumar OPCW ya fara gudanar da aikin kawar da dakunan ajiye makamai masu guba a kasar Syria. Dangane da haka, Mr Kerry ya bayyana cewa, wannan aiki na da muhimmanci sosai wajen warware batun makamai masu guba na kasar Syria. Wannan wani mafari ne mai kyau. Kuma kasar Amurka tana maraba da shi.
Haka kuma jami'an biyu sun bayyana cewa, za su yi shawarwari tare da wakilin musamman na MDD da kungiyar kawancen kasashen Larabawa Lakhdar Brahimi, da yin kokari wajen gduanar da taron kasa da kasa na biyu kan batun kasar Syria a tsakiyar watan Nuwamba na bana.
Ban da wannan kuma, Kerry da Lavrov sun tattauna kan batun nukiliya na kasar Iran. Inda bangarorin biyu suka nuna fatan za a samu kyakkyawan sakamako a shawarwari a tsakanin bangarori shida wato Amurka, Ingila, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, da kungiyar EU, da kuma kasar Iran a birnin Geneve dake kasar Switzerland a ranar 15 ga wata. (Zainab)