Mr. Bashar ya kuma bayyana cewa, tun da dadewa, kasar Syria ta shirya yin taron shawarwari a birnin Geneva, amma kasar Amurka da wasu kasashen da ke goyon bayan Amurka a yankin suka jinkirta da shi.
Da yake tsokaci kan batun makamai masu guba, shugaba Bashar ya nuna cewa, kasar ta fara sarrafa makamai masu guba tun a shekarar 1980s, amma ta riga ta dakatar da wannan aiki a karshen shekarar 1990s.
Ya ce, an riga an kawar da bukatun makamai masu guba a kasar tun farkon karni na 21, shi ya sa, a shekarar 2003, Syria ta gabatar wa kwamitin sulhu na MDD daftarin kawar da makamai masu guba a yankin Gabas ta Tsakiya, amma kasar Amurka ita ce ta hana fitar da daftarin.
Bugu da kari, ran 6 ga wata, cikin wata sanarwar da kungiyar sojojin Syria ta "Free Syrian Army" ta bayar, ta jaddada cewa, ba za ta yi shawarwari ba, har sai Bashar al-Assad ya sauka daga mukaminsa. Cikin sanarwar, kungiyar ta kuma yi kira ga bangarori daban daban da su cimma ra'ayi daya kan harkar. (Maryam Yang)