in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kira taron ministoci kan batun Syria a birnin London, in ji Birtaniya
2013-10-19 17:28:59 cri
A ranar Jumma'a 18 ga wata, ministan harkokin waje ta Birtaniya, William Hague ya yi shelar kira taron babban rukunin aminan Syria a ran 22 ga wata, inda za a yi shawarwari kan batun Syria da batutuwa masu alaka da taron Geneva karo na biyu.

Hague ya bayyana cewa, kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2118 ya yi kira da yin wani taron kasa da kasa kan batun Syria, a kokarin tabbatar da sanarwar Geneva da aka cimma a kwana nan, inda aka bukaci Syria da ta kafa hukumar rikon kwarya, wanda ya hada da membobin gwamnatin kasar, da na jam'iyyun adawa, da ma sauran kungiyoyi, ta hanyar yin shawarwari tsakaninsu. A kokarin cimma wannan buri, Birtaniya ta yanke shawarar jagorantar kiran taron da a kai wa lakabi da taron bangarori 11 na London, domin yin shawarwari kan share fagen kiran taron Geneva karo na biyu, ta yadda za ta nuna goyon baya ga hadaddiyar kungiyar jam'iyyun adawa na kasar Syria, da kokarin da wasu kasashen duniya suka yi da zummar kawo karshen rikicin Syria da cimma matsaya kan daidaita batun kasar a siyasance. Taron Babban rukunin aminan Syria, zai kunshi wakilan Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Masar, Jordan, Saudiya. Ragowar sun hada da Turkiya, hadaddiyar daular Larabawa, da kuma jam'iyyun adawa na kasar, wato hadaddiyar kungiyar jam'iyyun kasar Syria.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China