Wannan rukuni ya hada da masu bincike 20, da masu sarrafawa 15. Bayan saukarsa masauki, shugaban rukunin, kana darektan ofishin mu'amala da jama'a na kungiyar OPCW Wang Jun ya bayyana ma manema labarai cewa, yanzu ba za a bayyana irin aikin da za a yi ba.
Kafin wannan, kafofin yada labaru sun ba da labarin cewa, babban aikin rukunin shi ne tabbatar da yawan makamai masu guba da Syria take da su da kuma wurin da ta ajiye su. Amma bayan isowarsu a Damascus, 'yan rukunin za su gana da jami'an gwamnatin Syria tukuna, domin tattaunawa da su kan hakikanin abubuwa na ayyukansu.
Bisa wani kudurin da kungiyar OPCW ta zartas da shi a ran 28 ga watan Satumban bana dangane da lalata dukkan makamai masu guba na Syria, kamata ya yi wannan rukuni na farko ya isa Syria a ran a ga watan Oktoba domin kaddamar da aikinsa na yin bincike kan yanayin da ake ciki a fannin makamai masu guba a Syria. Kuma kudurin ya bukaci a kammala aikin lalata duk makaman da Syria take da su kafin tsakiyar shekarar 2014.(Fatima)