Valerie Amos ta bayyana cewa, a duk fadin kasar, jama'ar Syria suna fuskantar tashin hankali, kullum tana damuwa kan lamarin, kuma cikin watanni da dama da suka gabata, ba a samu ci gaba ko kadan ba kan aikin ba da agaji a wani garin da ke yankin karkarar babban birnin kasar, Damascus. Ko da yake mutane kimanin dubu 3 sun janye daga wurin, amma akwai mutane da dama ba su fita daga yankin ba.
Don haka, Valerie Amos ta yi kira ga bangarori daban daban da su cimma ra'ayi daya kan dakatar da musayar wuta a yankin, ta yadda hukumomin ba da taimakon jin kai za su iya shiga yankin don samar da ayyukan ceto. (Maryam)