Ofishin MDD dake birnin Damascus ya bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ya bayyana cewa, membobin rukunin bincike na MDD sun fara aiki kan batun yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria a ranar 27 ga wata. Ana sa ran cewa, rukunin zai kammala aikinsa a ranar 30 ga watan nan, daga baya zai rubuta wani rahoto game da wannan aiki, kuma za a gabatar da shi a karshen watan Oktoba.
Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar ta Syria na ci gaba da daukar matakan soja a birnin Damascus da yankunan dake dab da birnin. Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya bayar a ranar 27 ga wata, an ce, sojojin gwamnatin kasar sun kaddamar da hare-hare a gabashin al-Ghouta dake karkarar birnin Damascus da kuma kudancin karkarar birnin Damascus, inda suka harbe 'yan tawaye da dama, suka kuma raunata wasu, tare da murkushe sansaninsu, suka kuma lalata makaman da suke amfani da su. (Zainab)