Jiya Laraba 29 ga wata, an yi taron kasa da kasa kan rikicin kasar Sham a birnin Tehran hedkwatar kasar Iran, inda wakilai kimanin 40 daga kasashe da kungiyoyi daban-daban suka halarci taron domin fitar da wani shirin warware rikicin kasar Sham ta hanyar siyasa.
Ministan harkokin waje na kasar Iran, Ali Akabar Salehi ya bayyana cewa, jigon da aka bi a wannan karo shi ne neman wani shirin warware rikicin kasar Sham ta hanyar siyasa, da kuma taimakawa Sham wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ali Akabar Salehi ya ce, Sham ta kasance wata muhimmiyar kasa ce a yankin gabas ta tsakiya, don haka idan aka ci gaba da fama da wannan rikici, zai iya kawo illa sosai ga zaman lafiya da karko a yankin.
Jakadan kasar Sin dake kasar Iran Yu Hongyang a matsayin shugaban tawagar kasar, ya yi nuni a gun taron cewa, warware rikicin ta hanyar siyasa, ita ce hanya daya tilo da za a bi.
Sin na fatan kasa da kasa da za su taka rawa domin sa kaimi ga bangarori daban-daban na kasar Sham su daina bude wuta da fara yin shawarwari, mika mulki cikin lumana, gami da la'akari da moriyar kasa da jama'a bisa sanarwar da rukunin gudanarwa na taron ministoci da aka yi a birnin Genewa na kasar Switzerland ya bayar.
A wannan rana kuwa, ministan harkokin waje na kasar Sham Walid al- Moallem ya ce, ko shugaban kasar Bashar Al-Assad zai shiga babban zabe da za a gudanar a shekarar 2014 ko a'a, ya dangana ne da halin da ake ciki da kuma burin jama'a.
Walid al- Moallem kuma ya yi tir da sharuddan da kungiyar adawa ta yi na cewa a hambarar da Bashar kafin fara yin shawarwari, yana mai cewa, ba zai yarda da ko wani irin mataki da za a dauka wanda zai keta mulkin shugaba ba. (Amina)