Cikin wani jawabin da ya gabatar a ranar Jumma'a, shugaba Obama ya ce, rundunar sojin kasarsa na tattara bayanai kan batun kai hari da makamai masu guba da aka aiwatar a wajen birnin Damascus na kasar Sham, da nufin daukar dukkanin matakan da suka dace.
Bugu da kari, shugaban na Amurka ya ce, kasarsa na ci gaba da matsin lamba ga MDD, domin ganin an aiwatar da shirye-shiryen kare fararen hula daga hare-haren dake aukuwa, sakamakon yakin basasar kasar ta Sham. A sa'i daya kuma Amurka za ta tabbatar da hana yaduwar makamai masu guba a kasar.
Sai dai yayin da yake amsa tambayar wata kafar yada labarai, shugaba Obama ya nuna dari-dari ga batun kaiwa wata kasa hari, ba tare da cikakken goyon bayan MDD ba. Yana mai cewa, daukar irin wannan mataki na iya jefa shakku ga batun kiyaye dokokin kasa da kasa.(Saminu)