A makon jiya sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da ministan harkokin wajen kasar Iraki Hoshiyar Zebari sun yi ganawa a birnin Washington, fadar mulkin kasar Amurka, inda suka cimma ra'ayi daya cewa, bangarorin 2 za su kara hadin kai don hana Iran ta kai makamai ga kasar Sham ta jiragen sama, wadanda suke wucewa ta sararin saman kasar Iraki.
Saboda haka, kasar Amurka za ta samar da bayanan sirri ga Iraki, gami da sayarwa Iraki da makaman kare sararin sama da darajarsu ta kai kimanin dala biliyan 2.6, da kuma wasu jiragen saman yaki masu samfurin F-16 a nan gaba.
An ce, makaman da Iraki za ta samu suna kunshe da na'urorin hangen shawagi a sama, makamai masu linzami, da dai makamantansu. Yanzu haka kuma, kasar Amurka tana kokarin horar da masu tuka jiragen saman yaki na F-16 na kasar Iraki, kana za ta mika ma Iraki jiragen a shekara mai zuwa.
Da ma a cewar masu binciken al'amuran duniya, duk da cewa kasar Amurka tana baiwa kasar Iraki tallafin da ya kai fiye da dala biliyan daya a ko wace shekara, amma kasar tana kawance tare da kasar Iran, ko a fannin tattalin arziki ko kuma bangaren addini. (Bello Wang)