Morsi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Masar, jama'a da kuma sojojin kasar sun nuna goyon baya ga jama'ar kasar Syria a zabin da suka yi, kana ya jaddada cewa, kasarsa ba ta da yunkurin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasarta Sham.
Morsi ya nanata cewa, kasarsa ba ta goyon bayan dukkan wani aikin soja da na siyasa da sauran kasashen duniya da kungiyoyi suka yi a kasar Syria, kana ya yi kashedi ga kungiyar Hezbollah da ta dakatar da tsoma baki kan harkokin kasar Syria, ya kuma bukaci dakarun kungiyar da su janye daga kasarta Sham ba tare da bata lokaci ba.
Ban da wannan kuma, Morsi ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai don magance tsanantar halin da kasar Syria ke ciki, ya kalubalanci kwamitin sulhu na MDD da ya zartas da kudurin kafa yankin hana zirga-zirgar jiragen sama a kasar Sham. (Zainab)