An yi bikin mika ikon mallakar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da makamashin nukiliya, tsakanin jami'an kasar Iran da na kasar Rasha a ranar Litinin 23 ga watan nan, a birnin Bushehr dake kudancin kasar Iran. Matakin da ya baiwa kasar ta Iran cikakken ikon mallakar wannan tasha a hukunce, kuma za ta kasance irinta ta farko a kasar.
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA), ta shafe tsahon shekaru tana sa ido kan harkokin wannan tasha, don haka, ba a shakkun ayyukan da tashar ke gudanarwa ta fannin biyan bukatun fararen hula. (Amina)