A wannan rana, yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida kan batun nukiliya, shugaba Rouhani ya furta cewa, yin shawarwari hanya daya tak da za ta warware batun nukiliya na kasar. Iran za ta kokarta amincewa da shawarwari tsakaninta da sauran kasashe shida dangane da wannan batu, wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin, da kuma Jamus, a kokarin samun ci gaba a wannan fanni.
A game da batun kasar Syria kuma, shugaba Rouhani ya bayyana cewa, Iran bata amince da sauran kasashen duniya ba akan su tsoma baki a lamurran Syria, a ganin sa kamata ya yi jama'ar kasar su daidaita batun da kansu. Ban da haka, ya jaddada cewa, kafin babban zabe karo mai zuwa, gwamnatin Syria ta yanzu halalliyar gwamnati ce ta kasar, kamata ya yi kasa da kasa su amince tare da nuna mata girmamawa.
Game da dangantaka tsakanin Iran da Amurka kuma, Rouhani ya ce, kasashen biyu ba za su yi shawarwari tsakaninsu kai tsaye ba sai dai su girmama juna cikin adalci. Kamata ya yi Amurka ta amince da ikon amfani da makamashin nukiliya na kasar Iran tukuna, da daina sa baki cikin harkokin gida na kasar da kuma cire mata takunkumi. Ya kuma jaddada cewa, Iran ba za ta kawo gaban daukar matakai domin tsananta yanayin da ake ciki tsakanin kasashen biyu ba.