in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana zagaye na biyu na shawarwarin Alma-Ata game da batun nukiliya na kasar Iran
2013-04-05 16:41:18 cri
A ranar 5 ga wata, a birnin Alma-Ata, aka fara zagaye na biyu na zaman shawarwari game da batun nukiliya na kasar Iran, wanda ake yi tsakanin kasar Iran da kasashe 6 da batun ya shafa, wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus.

A wannan zama, za a tattauna ne kan martanin da Iran za ta bayar game da sabbin shawarwarin da kasashen 6 suka gabatar a baya.

Za a shafe kwanaki 2 ana zaman shawarwari, kuma za'a yi shawarwarin ne cikin siri. Sakataren hukumar tsaron koli na Iran kuma wakilinta a shawarwari na farko, Sayeed Jalili shine ya shugabanci tawagar kasar don halartar shawarwarin.

Haka kuma, babbar jami'ar kula da batun diplomasiyya da tsaro ta kungiyar EU Catherine Ashton ita ma ta halarci zaman shawarwarin, kuma tuni wato lokacin da take birnin Ankara ta yi kira ga kasar Iran da ta gabatar da martaninta game da sabbin shawarwarin da kasashe 6 suka bayar.

Daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga watan Febrairu ne aka yi zaman shawarwari na baya a birnin Alma-Ata, inda kasashe 6 suka gabatar da sabbin shawarwari.

Ko da yake, mahalartar zaman shawarwarin ba su fayyace abubuwan da ke kunshe a ciki ba, amma ana nuna yabo game da wadannan shawarwarin.

A ranar 3 ga wata, a gun taron manema labaru, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, yana fatan bangarori daban daban za su cimma matsaya guda, a yayin sabon zagaye na shawarwarin, kuma za a girmama batutuwan da ko wane bangare ke dora muhimmanci sosai a kai, don gaggauta daukar matakai wajen nuna amincewa da juna.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China