in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma Zhaoxu ya yi magana kan shawarwarin batun nukiliyar kasar Iran
2013-04-05 16:48:08 cri
Ranar 5 ga wata, kafin a fara shawarwarin zagaye na 2 tsakanin kasashe 6 masu alaka da batun nukiliya na kasar Iran da ma kasar a birnin Almaty na kasar Khazakstan, shugaban tawagar kasar Sin kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Ma Zhaoxu, a hirarsa da manema labarun kasar Sin, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu shawarwarin da ake yi a tsakanin kasashe 6 da kasar Iran ya shafi batutuwa masu zurfi da muhimmanci, don haka yana fatan bangarorin za su ci gaba da kokarin cimma matsaya daya.

Mista Ma ya yi kira da a nuna sassauci, da lura da abubuwan da dukkan bangarorin suke bukata, ta yadda za a iya daukar wasu takamaiman matakai wadanda za su taimakawa kokarin tabbatar da imani a tsakaninsu, da karfafa yanayin da ake ciki na shawarwari yadda ya kamata wanda ba a same shi cikin sauki ba, don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Mista Ma ya kuma nanata cewa, game da batun nukiliyar kasar Iran, kasar Sin ta dade tana nuna bukatar yin adalci da daukar nauyi, kana tana kokari matuka wajen bada hakuri na bukatar a zauna a yi shawarwari, a hakika ta taimaka wajen kiyaye da ciyar da shawarwarin da ake yi gaba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China