Bisa labarin da kafofin yada labaru na wurin suka bayar, an ce, Ashton ta aika da sako ga Hassan Rouhani don taya shi murnar zama shugaban kasar, kuma ta ce, ya samu cikakken goyon baya, kuma zai iya yin shawarwari da hadin gwiwa da kasashen duniya, don gaggauta warware shirin nukiliya na kasar Iran.
A cikin wasikar, Ashton ta ce, a shirye take don ci gaba da yin shawarwari, kuma tana fatan gaggauta shirya taron tattaunawa mai ma'ana da rukunin shawarwari na kasar Iran.
A ranar 4 ga wata, Rouhani ya yi rantsuwar kaman aiki, a matsayin shugaban kasar Iran na 11. A ranar 6 ga wata, a birnin Tehren Rouhani ya bayyana cewa, Iran tana fatan gaggauta farfado da shawarwari kan batun nukiliya na kasar cikin tsanaki. Amma ya jaddada cewa, tace sinadarin uranium hakkin kasar Iran ne, Iran ba za ta daina wannan aiki ba, kuma Rouhani ya ce, ba zai kawar da yiwuwar yin shawarwari kai tsaye da kasar Amurka ba.(Bako)