Wannan cibiyar dai mai suna Shahid Rezaeenejad da aka kaddamar a ranar Talatan nan 9 ga wata a tsakiyar garin Ardakan a gundumar Yazd, kuma gidan talabijin din kasar suka nuna kai tsaye, Shugaban kasar Mahmoud Ahmadinijad ya halarci bikin abin da ya zo daidai da ranar kasar na fasahar makaman nukiliya.
A jawabinsa Shugaba Ahmadinajad ya ce kasar ta samu ci gaba sosai duk da hassadar makiya ta bangaren siyasa da kuma takunkumin da ake ta saka mata.
A ranar Talatan ne kasar dake karkashin addinin Islama ta kuma kaddamar da wani cibiyar a Saghand shi ma na sarrafa sinadarin uranium din duka a gundumar Yazd wanda ake sa ran zai iya hako sinadarin daga nisan mita 350 daga karkashin kasa.
Mahukuntar kamfanin dillancin labarai na kasar IRNA sun bada rahoto a jiya Litinin cewa sinadarin uranium din da aka hako za'a sarrafa shi zuwa garin Yellowcake wato garin uranium mai kauri a cibiyar Shahid Rezaeenejad. (Fatimah)