A wannan rana, Najafi ya yi bayani game da batun nukiliya na kasar Iran karo na farko a gun taron kwamitin hukumar IAEA, inda ya ce, a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, Iran za ta sauke nauyin da ke wuyanta, da bayyana shakkun da aka nuna mata game da batun nukiliya, kuma za ta hada gwiwa da hukumar IAEA cikin sahikanci don daddale shirin kafa tsarin yin bincike.
Wakilinn kasar ta Iran a sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, kasar sa zata raya shirin nukiliya domin zaman lafiya, kuma bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, yace Iran tana da hakkin raya nukiliya don zaman lafiya, kuma ba zai yi sassauci game da wannan batu ba.
Najafi ya kuma bayyana cewa, Iran a shirye take, don tsara wani shirin yin shawarwari game da batun nukiliya na kasar cikin dogon lokaci, bisa tushen girmama juna da moriyar juna, amma ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su daina kawo kalubale ko saka takunkumi, sannan su girmama kasar Iran yadda ya kamata.
A gun taron kwamitin da aka yi a ran nan, wakilin kasar Amurka a hukumar IAEA Joseph E. Macmanus ya ce, kasar Iran ta yi amfani da shirin kafa wani tsari don kawo jinkiri game da aikin bincike, kuma ya bukaci Iran da ta daina yin wasan dabarun jinkiri, ta hadin gwiwa da hukumar IAEA daga duk fannoni, ta kuma amince da binciken da za a yi mata.
A sa'i daya kuma, Joseph E. Macmanus ya jaddada cewa, idan ba a samu takamaiman ci gaba ba a gun taron kwamiti na karo mai zuwa, Amurka da sauran mambobin kwamitin za su dauki tsattsauran matakan diplomasiyya don yin matsin lamba ga kasar Iran.(Bako)