Hassan Rouhani ya lashe zaben kasar ta Iran ne da aka kada a ran 14 ga watan Yulin da ya gabata da kuri'un da yawansu ya kai kaso 50.7 bisa dari. Sabon shugaban kasar ta Iran da ake gani a matsayin mai matsakaicin ra'ayi zai dora ne daga inda shugaba Ahmadinejad ya tsaya, zai kuma gaji tarin matsalolin tattalin arzikin da kasar take fama da su yanzu haka, tare da tsantsamar dangantakar dake tsakanin kasar ta Iran da kasashen yanmacin duniya.
Ana zaton sabon shugaban zai kaddamar da majalisar zartaswarsa yayin bikin rantsuwar na ranar Lahadin nan, ko da yake yana iya yin hakan nan da makwanni 2 masu zuwa. (Saminu)