in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban kasar Iran zai ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasarsa da sauran kasashe bisa tushen girmama juna
2013-06-16 16:46:03 cri
A ranar 15 ga wata, sabon shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa tushen girmama juna, tare da tabbatar da samun zaman lafiya da tsaro da kuma bunkasuwa a yankinta da ma dukkanin fadin duniya. Kana ya yi kira ga kasa da kasa da su girmama da amincewa da hakkin kasar Iran, da yin shawarwari tare da Iran yadda ya kamata.

A wannan rana, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da wata sanarwa ta hanyar kakakinsa, inda ya taya Hassan Rohani murnar cimma nasara a zaben shugaban kasarta Iran karo na 11. Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya baiwa zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 14 ga wata cikakken muhimmanci, ya kuma nuna gamsuwa ga samun kuri'u mafiya yawa da dama a wannan karo. Ban Ki-moon ya bayyana burin ci gaba da yin kokari tare da shugabannin kasar Iran wajen warware manyan batutuwan kasa da kasa da kuma bada moriya ga jama'ar kasarta Iran. Kana ya ce, zai ci gaba da sa kaimi ga kasar Iran don ganin ta taka muhimmiyar rawa kan harkokin yankinta da na duniya gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China