in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya kai ziyara a kasar Iraqi
2013-09-09 15:54:48 cri
A ranar 8 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad javad zarif ya isa birnin Bagadaza, don kai ziyarar aiki a kasar Iraqi.

Ziyarar Zarif a kasar Iraqi, ta kasance ziyara ta farko da ya yi bayan da ya hau mukamin sabon ministan harkokin wajen kasar Iran. A ranar 8 ga wata, Zarif da firaministan kasar Iraqi Nuri Kamal al-Maliki sun tattauna halin da ake ciki a kasar Siriya da dangantakar da ke tsakanin kasashen Iran da Iraqi, kuma sun yi kira da a inganta hadin gwiwa don magance kalubale a wannan yanki. A nasa bangare, Maliki ya jaddada cewa, gwamnatin Iraqi ta dukufa ka'in da na'in wajen warware rikicin Siriya cikin ruwan sanyi, sabo da wannan ba ma kawai zai amfanawa bangarorin daban daban na kasar Siriya ba, har ma zai amfana wa sauran kasashen da ke yankin Gabas ta tsakiya.

A gun taron manema labarai na hadin gwiwa tsakaninsa da ministan harkokin wajen kasar Iraqi Hoshyar Zebari, Mr. Zarif ya bayyana cewa, bisa kundin tsarin mulki na M.D.D., yin shisshigin soji ga kasar Siriya laifi ne na keta doka, ya ce, bai kamata wasu mutanen su goyi bayan bangaren 'yan hamayya na Siriya ba, a sa'i daya kuma ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya riga ya taka tarkon yakin Siriya da wasu mutane suka dana, yana fatan Shugaban Obama zai yi la'akari da moriyarsa da ma moriyar na duk wannan yanki gaba daya, don kaucewa wannan tarko.

A nasa bangare shi ma, Mt. Hoshyar Zebari ya ce, Iraqi ba za ta zama wurin da za a afka wa kasar Siriya da yaki ba, kana ba za ta taimaka wa sauran kasashe a wannan fanni ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China