A wannan rana, an yi taron sauraron bayanin kwamitin sulhu na MDD kan takunkumin da aka sanyawa kasar Iran. Yayin da yake jawabi, Wang Min ya nuna cewa, kamar yadda kasar Sin ta taba nunawa, ya kamata a warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. Kuma kasashen nan shida da batun ya shafa sun jadadda cewa, suna fatan za a iya warware matsalar sannu a hankali ta hanyar shawarwari daga dukkan fannoni, bisa tushen girmamawa juna da kuma adalci.
Wang Min ya kuma kara da cewa, kasar Sin ba za ta amince da daukar matakan amfani da makamai, ko yin barazana wajen warware matsalar ba, kuma bai kamata a matsa wa Iran lamba fiye da kima da sanyawa kasar Iran karin takunkumi ba. Har ila yau ya ce, a halin yanzu, ya kamata a dauki matakin fara sabbin shawarwari tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa cikin sauri, kuma ya dace kasar Iran da hukumar kula da harkokin nukiliya ta kasa da kasa, su inganta hadin gwiwa da shawarwari da ke tsakaninsu, domin cimma daidaito kan wasu matsalolin da har yanzu ba a warware su ba cikin hanzari. (Maryam)