in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara kada kuri'ar zaben shugaban kasar Iran
2013-06-14 15:36:51 cri

An fara kada kuri'un zaben shugaban kasar Iran karo na 11 a ran 14 ga wata da misali karfe 8 na safe, agogon wurin, inda babban jagoran kasar Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya kada kuri'a ta farko a rumfar da aka kafa a fadar shugabanni dake birnin Tehran.

Za a zabi sabon shugaban kasar daga 'yan takara shida, da suka kunshi sakataren kwamitin tsaron kasar Iran kuma wakilin farko kan shawarwarin nukiliya Sayeed Jalili, magajin birnin Tehran Mohammed Baqer Kalimbav, tsohon ministan harkokin waje Ali-akbar Velayati, tsohon wakilin farko kan shawarwarin nukiliya Hassan Rouhani, tsohon babban kwamandan rundunar tsaron kasa ta juyin juya hali ta Iran Mohsen Rezaei, da kuma tsohon ministan sako da sadarwa Mohammad Gharazi.

Bisa kididdigar da hukumar harkokin cikin gida ta kasar Iran ta bayar an ce, masu zabe kimanin miliyan 50.5 ne za su jefa kuri'unsu a rumfunan zabe dubu 60 da aka kafa a fadin kasar. Za a kammala wannan aiki a wannan rana, kuma an kiyasta cewa, za a gabatar da sakamako a ran 15 ga wata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China