in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 62 sun mutu sakamakon harin da aka kai a kasar Kenya
2013-09-24 15:01:30 cri

Har zuwa lokacin da aka ruwaito wannan labari, sojojin kasar Kenya da 'yan tawaye suna ci gaba da arangama da juna bayan aukuwar hari na fiye da kwanaki biyu da aka kai a wani babban shagon dake birnin Nairobi na kasar Kenya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane har 62.

Hukumar harkokin gida ta kasar ta sanar a ran 23 ga wata cewa, an kusa kammala aikin ceto. 'Yan sanda kasar sun nuna cewa, bisa sakwannin da aka bayar an ce, 'yan tawaye dake boye cikin wannan babban shago sun fito daga kasashe daban-daban, hakan ya sa lamarin ya zama wani rikicin ta'addanci da ya shafi kasa da kasa.

Tun tuni, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Kenya ta sanar da cewa, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane 68, amma daga baya ta ce, akwai kuskure wurin kirga gawawwaki. Bisa labarin da aka bayar, wadanda suka rasa rayukansu sun fito ne daga Kenya, Birtaniya, Faransa, Canada da dai sauran kasashe. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China