in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi kiran a nuna matukar hakuri a Masar
2013-08-16 10:02:55 cri

A ranar Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi kira ga dukkan bangarori a kasar Masar da su nuna matukar hakuri a kuma kawo karshen tashin hankali a kasar ta yankin gabas ta tsakiya bayan mutane 500 sun rasa rayukansu sakamakon arangama tsakanin dakarun tsaro da masu zanga zanga dake neman a mayar da hanbararren shugaban kasar Mohammed Morsi.

Wakiliyar din din din ta kasar Argentina a MDD Maria Cristina Perceval wacce ita ce ke rike da shugabancin karba karba na kwamitin a watan Agusta ita ce ta baiyana hakan, yayin da take ganawa da 'yan jarida bayan wata ganawa da aka yi ta sirri dangane da halin da ake ciki yanzu a kasar Masar.

Ta ce, ra'ayin mambobin wannan kwamiti shi ne ya kamata a kawo karshen rikici a kasar Masar, kana dukkan bangarori su nuna hakuri.

Magatakardan MDD Ban Ki-moon wanda ke ziyara a yankin gabas ta tsakiya a halin yanzu ya yi suka da kakkausar murya ga rikici da ya taso sakamakon ayyukan, tare da yin kira ga dukkan bangarorin kasar Masar su sake nazarin matakansu bisa la'akari da yanayin siyasa da ake ciki a yanzu, domin ceto kasar daga abkawa cikin mummunan hali. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China