Amma, har zuwa yanzu, gwamnatin kasar ta Guinea ba ta fitar da sabon jerin sunayen wadanda suka rasa rayukan nasu yayin ricikin ba. Sai dai rahotanni na baya sun bayyana cewa mutane 16 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, inda kuma wasu 80 suka jikkata. Wannan dai yanki na Nzerekore na da nisan kilomita dubu 1 ne da babban birnin kasar ta Guinea, yana kuma yankin kudu maso gabashin kasar.
An dai ce ranar 15 ga wata, wani dan sanda dan kabilar Guerze ya harbe wani direba dan kabilar Konianke, yayin da ake tsaka da takaddama kan zargin sace wani abu, matakin da ya harzuka 'yan kabilar wanda aka harbe, inda nan take suka fara daukar fansa, wanda hakan ne ya haddasa barkewar rikicin da ya janyo asarar rayuka da dama tsakanin 'ya'yan kabilun biyu. (Maryam)