in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta ce, a shirye take ta ba da gudummawar warware rikici a Masar
2013-07-05 09:54:29 cri

Kungiyar hadin kan kasashen Afirka mai mambobi 54, (AU) ta bayyana ranar Alhamis cewa, a shirye take ta ba da gudummawarta wajen samo hanyar warware rikici da ake fuskanta a kasar Masar wacce mamba ce ta kungiyar.

Wata sanarwa daga shugabar hukumar gudanar da kungiyar AU Nkosazana Dlamini Zuma na mai bayyana cewa, kungiyar ta AU tana lura da yadda abubuwa ke wakana a Masar.

Tana nuna damuwa, musamman ma dangane da zaman tashin hankali a cikin kasar da kuma abin da rikicin ke iya haifarwa.

Shugabar har ila yau ta yi nuni da bukatar yin tattauanawa tsakanin daukacin masu ruwa da tsaki na kasar Masar, domin a samu warware rikicin.

Ta ce, akwai bukatar kiyaye nasarorin da aka cimma a kasar bayan juyin juya hali na shekarar 2011, da ma na tsarin demokradiyya, ta hanyar cimma wata matsaya dangane da makomar kasar.

Shugabar na shirin tura wata tawagar manyan mutane zuwa kasar Masar, da zaran an samu damar hakan domin yin shawarwari da masu ruwa da tsaki, da kuma taimakawa wajen fara zaman tattaunawa mai inganci. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China