Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya ya sanar a ran Lahadi 22 ga wata cewa, wani Basine ya mutu a cikin wannan harin. Ban da haka, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a wannan ranar cewa, Sin ta dauki matsayin yaki da kowane irin ta'addanci, tare kuma da yin Allah wadai da harin da aka kai a Kenya, dadin dadawa, ya nuna juyiyi sosai ga mamata tare da mika ta'aziyya ga iyalansu. Ya ce a matsayin kawar kasar Kenya, Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da Kasar take yi wajen tabbatar da tsaronta da zaman karko a yankin.
Bayan harin da aka kai wa kasar Kenya, babban sakataren MDD Mr Ban Ki-Moon, kwamitin sulhu na MDD, kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, da kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Canada da dai sauran kasashe sun ba da sanarwa don yin tir da harin da aka kaiwa fararen hula a kasar Kenya, tare kuma da mika ta'aziyyarsu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. (Amina)