in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amfani da hanyar siyasa ita ce mafita ga rikicin Masar, a cewar Ban Ki-moon
2013-08-07 10:31:16 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana a ranar Talata cewa, hanya daya dilo ta warware rikicin kasar Masar, ita ce amfani da tsarin siyasa cikin zaman lafiya.

Kakakin MDD Martin Nesirky, ya shaidawa taron manema labarai cewa, yayin wata zantawa da Mr. Ban ya yi da ministan harkokin kasashen wajen kasar ta Masar Nabil Fahmy, ya bukaci mahukuntan kasar Masar, da su tabbatar da kare 'yancin Misirawa baki daya tare da kawo karshen duk wani tashin hankali.

Bugu da kari, kakakin nasa ya ce, babban magatakardan MDD ya nanata kiransa na sakin hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi, inda ya bukaci shugabannin kasar Masar, da su bullo da wata hanyar sasantawa mai inganci, ya kuma tunatar da su game da nauyin da ke kansu game da alkiblar makomar Masar nan gaba.

Rikicin kasar ta Masar ya yi kamari ne a ranar 3 ga watan Yulin, lokacin da sojojin kasar ta Masar suka hambarar da Morsi daga karagar mulki, lamarin da ya haifar da zanga-zanga, kana daga bisani aka jingine kundin tsarin mulkin kasar tare da kafa gwamnatin wucin gadi.

Sakamakon rikicin siyasar da ake fama da shi a kasar Masar, ya sa Ban Ki-moon da babbar kwamishinar kula da kare hakkin bil-adama ta MDD Navi Pillay, suke ta yin kira ga mahukuntan kasar da su mutunta doka da ka'idojin kare hakkin bil-adama na kasa da kasa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China