in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta ce, a shirye take na taimakawa shirin siyasa da zai rage tashin hankali a Masar
2013-08-09 10:08:12 cri

Ministan harkokin wajen kasar Faransa, mista Laurent Fabius ya kara jaddadawa a ranar Alhamis cewa, kasarsa a shirye take na taimakawa duk wani shirin da zai kawo rage tashe-tashen hankali da kuma taimakawa ga kafa tsare-tsaren demokaradiyya na mika mulki ga fararen hula a kasar Masar, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa a cikin wata sanarwa.

Mista Fabius ya samu tattaunawa a ranar Alhamis tare da bangarori daban daban da wannan rikcin siyasa na kasar Masar ya shafa tare da bayyana cewa, hanyar samun wata masalha ita ce bangaorin dake gaba da juna su amince da yin shawarwari domin cimma daidaito, maimakon kara ruruwa wutar gaba da tashe-tashen hankali, in ji wannan sanarwa.

A gaban mista Nabil Fahmy, ministan harkokin wajen kasar Masar, jami'in diplomasiyar kasar Faransa ya ce, kasarsa a cikin shiri take na taimakawa ko bullo da wata hanyar da za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin siyasa a wannan kasa dake arewacin nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China