in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 19 ne sun mutu a sakamakon abkuwar rikici a Masar
2013-07-27 16:45:18 cri

Daga daren ranar 26 zuwa safiyar ranar 27 ga wata, bisa agogon wurin, an yi babbar zanga-zanga a wurare daban daban na kasar Masar, inda a kalla mutane 19 suka mutu, sakamakon abkuwar rikicin nuna karfi, yayin da wasu mutane sama da dari daya suka jikkata.

A daren wannan rana, bisa kiran ministan tsaron kasar Masar, Abdul Fatah al-Sisi, mutane da yawa sun yi zanga-zanga a tituna, domin ba da goyon baya ga sojoji wajen yaki da nuna karfi da ta'addanci. A sa'i daya kuma, kungiyar 'yan uwa musulmi, wato Muslim Brotherhood da magoya bayan tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi suna ci gaba da zanga zanga, inda suka bukaci a maido da matsayin Morsi na shugaban kasar Masar.

A safiyar ranar Asabar 27 ga wata, bisa agogon wurin, magoya bayan Morsi sun yi fito-na-fito da 'yan sanda a birnin Nasr dake gabashin Alkahira, inda bangarorin biyu sun jefa duwatsu da barkonon tsohuwa ga juna. Daga bisani, wasu da ba a san ko su wane ne ba sun harbe masu zanga-zanga. Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na MENA ya samu daga asibitocin dake dab da wurin a ran 27 ga wata, an ce, mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu kimanin dari biyar suka jikkata a sakamakon haka. Ban da haka, kamfanin dillancin labaru na MENA ya samu labari daga hukumar tsaron kasar Masar cewa, 'yan sanda 7 sun ji rauni a daren ranar 26 ga wata. Bugu da kari, hukumar tsaron ta kara da cewa, an cafke membobin kungiyar 'yan uwa musulmi 53 a daren wannan rana, wadanda ake tuhumarsu da aikata laifin daukar makamai a yayin zanga-zangar.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a lokacin zanga-zangar, magoya bayan Morsi suna yunkurin katse zirga-zirgar motoci a wata gadar ta 6th of Oktoba, da kafa tantuna a gaban ginin tunawa da jarumai a birnin Nasr, amma ba su cimma nasara ba a sakamakon yunkurin 'yan sanda. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Masar ta bayyana a wata sanarwar cewa, 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa kawai a cikin rikicin, ba tare da harbe masu zanga-zanga ba.

Amma bisa labarin da gidan talibijin na Al Jazeera ya bayar, an ce, masu zanga-zanga 75 sun mutu cikin rikicin, yayin da wasu mutane sama da dubu daya sun jikkata. Amma wannan labari bai samu tabbatawar ma'aikatar kiwon lafiya ko manyan kafofin yada labaru na Masar ba.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China