in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta cimma nasarar harba tauraron dan Adam mai bincike yanayin sama
2013-09-23 16:36:16 cri

Yau Litinin 23 ga wata, da karfe 11 da minti 7 na safe a cibiyar harbar kumbuna ta Taiyuan, Sin ta harba wani tauraron dan Adam mai bincike yanayin sama karo na uku mai suna "Feng Yun 3" ta hanyar yin amfani da roka Changzheng ta hudu mai dauke da kumbo mai lamba uku.

Wannan tauraro zai hade da sauran tauraro biyu da aka harba tun da farko a wannan fanni, wadanda za su kara karfi wajen bincike yanayin sama da yin rigakafi.

Wannan tauraro zai yi bincike kan yanayin sama na tsawon awowi 24 a jere, musamman ma zai samar da ma'aunin yanayin sama tare kuma da sa ido kan bala'u daga Indallahi, a sa'i daya kuma, zai samar da bayanai a kan sauyin yanayi da ba da taimako ga sufuri a sama da teku.

Tauraro irin wannan guda biyu da aka harba su a watan Mayu na shekarar 2008 da watan Nuwamba na shekarar 2010, wadanda suke gudanar da ayyuka yadda ya kamata, bayan da suka hada da na uku kuma za su kara karfin sa ido kan yanayin sama da yin rigakafi a wannan fanni sosai.

An ba da labari cewa, wannan ya kasance karo na 181 ke nan da aka yi amfani da roka Changzheng. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China