in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta harba sabon tauraron dan Adam
2013-02-28 20:20:32 cri
Kakakin ofishin shirin kula da harkokin tauraron dan Adan na kasar Sin, ya fada cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa, kasar Sin za ta harba sabon tauraron dan Adan din da kasar ta kera a wani lokacin cikin watan Yuni da kuma Agusta.

A cewar sanarwar, za a harba tauraron samfurin Shenzhou mai lamba 10 tare da 'yan sama jannatin kasar guda uku, wanda ake saran zai hade da tauraron dan-adam sanfurin Tiangong mai lamba 1 da aka harba a kwanakin baya.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Satumban shekarar 2011 ne aka harba tauroran na Tiangong mai lamba 1, kana daga bisani ya hade da tauraron dan-adan sanfurin Shenzhou mai lamba 8 wanda ba matuki a cikinsa a watan Nuwamban shekara ta 2012 da kuma na Shenzhou mai lamba 9 da dan-adan ke sarrafa shi a watan Yunin shekara ta 2012.

Sanarwar ta ce bayan an shafe tsawon shekaru ana gudanar da gwaji, sabon tauraron dan-adam din da za a harba, zai kasance tauraron dan-adam na farko da dan-adam ke sarrafa shi da Sin za ta harba.

Bisa ga tsare-tsaren da aka yi, manufar harba wannan tauraron dan-adam sun hada da nazarin aikin hadewar taurarin, karfin tsarin hadewar na'urorin wajen tallafawa tsarin aiki da kuma harkokin rayuwa, da kuma kwarewar 'yan sama jannatin wajen tafiyar da aikinsu.

Bugu da kari, za a kammala binciken da ake kan 'yan sama jannati game da sabawa da yanayin sararin samaniya, baya ga gwajin yin gyara ga taurarin dan-adam din da sauran muhamman bangarorin kimiya da ake bukata wajen bunkasa tashar sararin samaniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China